By G9ija

Yayin da batun tsayar da Musulmi da Musulmi a takarar shugabancin Najeriya da jam’iyyar APC ta yi ke ci gaba da jan hankula, wata kungiyar mabiya addinin Kirista da ke goyon bayan APC ta sha alwashin ba da gudunmawa ga takarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023.

Ƙungiyar ta Christian Northern Najeriya Political Forum ta yi haka ne duk da irin adawar da Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN ke yi da wannan lamari.

Shugabannin ƙungiyar sun bayyana goyon bayan nasu ne a Kaduna a wani taro da suka yi da wasu jagorori na jam’iyyar.

Haka kuma ƙungiyar ta ce ta yi haka ne a ƙoƙarin da take yi na kauce wa duk wani tarnaki da ka iya kawo cikas ga ɗan takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin inuwar APC’n a zaɓen 2023.

Commando Mohammad Barau, shi ne shugaban ƙungiyar kuma ya bayyana cewa za su zaɓi Tinubu sakamakon suna ganin shi ne kaɗai zai iya ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta a ciki.

“Yanayin da muka shiga ciki ya kamata mu duba ba wai maganar Muslim-Muslim ba, mu Kiristoci ana cewa ba za mu yi APC ba, to mu APC muke ciki kuma APC za mu yi.

“A matsayina na Kirista ina da ra’ayin da zan iya zaɓe, shugabana na CAN yana da na shi ra’ayi da zai iya fadi, ra’ayi ne fa siyasa, muna wahala a Jam’iyyar APC, ƙa’ida ne kuwa mu kai ƙarshen wahalarmu a Jam’iyyar APC domin kuwa mun san za mu tsinci wani abu a jam’iyyar nan,” in ji Barau.

“Allah shi ne sheda, babu wanda wani daga cikin magoya bayan Asiwaju ya yi wa magana, su ne suka zauna suka ƙirƙiri ƙungiyar ta su kuma suka ga cewa lallai ya zama musu wajibi su bayar da gudunmawa domin gina sabuwar Najeriya,” in ji Ibrahim Masari.

A ƴan kwanakin nan ne dai wasu shugabannin ƙunigiyar Kiristoci ta Najeriya suka fito inda suka nesanta kansu da sanya sunayen wasu mambobin kungiyar a kwamitin yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu, matakin da ga bisa dukkan alamu bai kwanta wa wasu yaƴan ƙungiyar ta CAN ba